Yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah. Tsira da amincin Allah su tabbata ga annabin rahama, annabinmu Muhammadu da alayensa da sahabbansa da waxanda suka bi tafarkinsa har zuwa tashin qiyama. Bayan haka:
Ya ku bayin Allah. Ubangiji mai girma da buwaya ya horewa bayin hanyoyi daban daban don samin gidan aljannah domin tsananin tausayinsa ga bayinsa.
Allah yana faxa a cikin littafin mai tsarki cewa:
{ุฅูููู ุงูููููู ุงุดูุชูุฑูู ู
ููู ุงููู
ูุคูู
ูููููู ุฃูููููุณูููู
ู ููุฃูู
ูููุงููููู
ู ุจูุฃูููู ููููู
ู ุงููุฌููููุฉู ููููุงุชูููููู ููู ุณูุจูููู ุงูููููู ููููููุชูููููู ููููููุชูููููู ููุนูุฏูุง ุนููููููู ุญููููุง ููู ุงูุชููููุฑูุงุฉู ููุงููุฅูููุฌูููู ููุงููููุฑูุขููู ููู
ููู ุฃูููููู ุจูุนูููุฏููู ู
ููู ุงูููููู ููุงุณูุชูุจูุดูุฑููุง ุจูุจูููุนูููู
ู ุงูููุฐูู ุจูุงููุนูุชูู
ู ุจููู ููุฐููููู ูููู ุงููููููุฒู ุงููุนูุธููู
ู} [ุงูุชูุจุฉ: 111]
(Lalle Allah ya sayi rayukan muminai da farashin aljanna. Su yi yaqi don xaukaka kalmar Allah, sai su kashe kuma a kashe su. Wannan alkawari ne na gaskiya da ya xaukarwa kansa a cikin Attaurah da Linjila da Alqur'ani. Wanene wanda ya fi Allah cika alkawarinsa?! Don hka ku yi murna da wannan ciniki da kuka yi da Allah. Wannan kuma shi ne babban rabo
An karvo daga Jarir xan Abdullahi ya ce: Mun kasance a wani lokaci a wajen Manzon Allah da daddare, wata yana tsakiyar haskensa, sai Manzon Allah ya ce: โHaqiqa za ku ga Ubangijinku, a fili kamar yadda kuke ganin wannan watan a wannan lokaci, ta bare da turereniya ย ba. Saboda haka duk kada xayanku ya yarda a fi qarfinsa akan sallar Asuba da ta Magariba". [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].
Manzon Allah ya ce: โDuk wanda ya yi sallar nafila rakaโa goma sha biyu a yini da dare, Allah zai gina masa gida a aljanna. Rakaโa biyu kafin asubahi. Rakaโa huxu kafin azahar da rakaโa biyu a bayanta, da rakaโa biyu bayan sallar magariba da rakaโa biyu bayan sallar ishaโi". Muslim ne ya ruwaito shi.
A game da qiyamullaili, Allah yana cewa;
{ุชูุชูุฌูุงููู ุฌููููุจูููู
ู ุนููู ุงููู
ูุถูุงุฌูุนู ููุฏูุนูููู ุฑูุจููููู
ู ุฎูููููุง ููุทูู
ูุนูุง ููู
ูู
ููุง ุฑูุฒูููููุงููู
ู ููููููููููู} [ุงูุณุฌุฏุฉ: 16]
(Jukkunansu suna nisa da shimfixinsu. Suna bautawa Ubangijinsu suna masu tsoron azabarsa, masu kwaxayin ladansa. Kuma suna ciyarwa daga abin da muka azurta su). Shi ya sa Manzon Allah yake cewa: โKu yaxa sallama a tsakaninku. ku ciyar da abinci, ย ku sada zumunci, ku yi sallah da daddare lokacin da mutane suke barci, sai ku shiga aljanna da aminci". [Tirmizi ne ya ruwaito].
www.islamkingdom.com/ha/fagen-imani-wuta-da-aljanna